Najeriya za ta sake karbar magungunan cutar kuturta
March 8, 2025Talla
Tun a farkon shekarar da ta gabata ne dai bayanai suka nuna yadda Najeriyar ke fama da karancin magungunan kashe kwayoyin cutar ta kuturta, saboda matsaloli na tsare-tsare daga hukumar.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta danganta jinkirin da matsaloli na gwaje-gwaje masu inganci da ma wasu masu nasaba da tsarin gudanarwa.
Ana dai sa ran magungunan cutar ta kuturta, za su isa kasar ta Najeriya ne a wannan Lahadi.
Najeriyar da ke kan gaba ta fuskar yawan al'uma a nahiyar Afirka, na samun sama da mutum dubu guda da ke kamuwa da cutar kuturtan a duk shekara.
Kasashe 12 ne dai na duniya ke fama da cutar da suka hada da Najeriya da Brazil da Indiya da Bangaladesh, inda a kowace shekara ake samun masu kamuwa daga dubu daya har zuwa mutum dubu goma.