Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutane 33 a jihar Zamfara
July 28, 2025Wasu 'yan bindiga sun halaka mutane 33 daga cikin sama da 50 da aka yi garkuwa da su a kauyen Banga da ke jihar Zamfara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, duk da biyan kudin fansa na fiye da Dala 30,000 da aka yi. Shugaban karamar hukumar Kauran Nomada Mannir Haidara ya tabbatar da kashe wasu da aka yi garkuwa da su, amma bai bayar da takamaiman adadi ba.
Karin bayani: Biyan kudin fansa na zama matsala a Najeriya
Sai dai babban jami'in ya ce mutane 18 da 'yan bidiga suka sako na samun kulawa saboda munanan raunukan da suka yi musu sakamakon duka. Tun a watan Fabrairu ne, wasu ‘yan bindiga a kan babura suka mamaye kauyen Banga tare da yin garkuwa da mutane 51, ciki har da mata masu juna biyu, bayan da suka kashe wasu biyu, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.
Karin bayani: A Najeriya 'yan bindiga sun tashi kauyuka da dama
Dama dai, Zamfara na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da 'yan ta'addanci da 'yan fashi, wadanda ke kai munanan hare-hare a kauyuka, da sace mutane domin neman kudin fansa. Sai dai bullar kungiyar Lakurawa ya kara ta'azzara tashe-tashen hankula a yankin, lamarin da ya tilasta wa gwamnatocin jihohin da abin ya shafa daukar matakan dakile ‘yan bindiga.