Najeriya: Wasu alkalai za su fuskanci kora
October 4, 2018Hukumar ta ce daya daga cikin alkalan James Agbadu-Fishim ya yaudari jama'a inda ya rika karbar kudi daga hannun lauyoyi da kuma mutane wadanda ke da kararraki a gabansa inda ya yi musu karyar cewa mai dakinsa ta rasu kuma ya na cikin zaman alhini da damuwa.
Hakan nan kuma hukumar kula da da'ar alkalan ta bada shawarar sallamar wata mai shari'ar Rita Ofili-Ajumogobia bayan da ta tabbatar da cewa wasu jami'an gwamnati sun zuba mata kudi a asusunta na ajiya a Banki. Ba a dai baiyana adadin kudaden ba.
Tuni aka dakatar da alkalan biyu kafin shugaba Muhammadu Buhari ya yanke hukunci akansu. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa Transparency International ta sanya Najeriya a matsayi na 27 a jadawalin kasashe da suka yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa a duniya a 2017.