Najeriya: Wani soja ya harbe abokin aikinsa
November 18, 2022Talla
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya a yankin Samson Nantip Zhakom ne ya tabbatar da wannan labarin, inda ya ce lamarin ya auku ne a jiya Alhamis kuma ma tuni sojin da ke barikin a lokacin da abin ya faru suka bindige shi kafin ya kai ga sauran jama'a.
Ya zuwa yanzu dai ba wata sanarwa da aka samu daga jami'an sojin kasar kan dalilin da ya sanya sojan ya bude wuta amma kuma sojin sun ce suna gudanar da bincike.