Sojojin Najeriya sun zubar wa mata ciki
December 8, 2022Koda yake rundunar tsaro ta Najeriya ta musanta wannan zargi, wanda ta ce kamfanin dillancin labaran na Reuters na neman haddasa husuma ne da kuma shafa mata kashin kaji. A cewar rahoton na Reuters dai, an zubar da cikin matan da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi mus shi ta hanyar auren a dole ko kuma fyade sama da dubu 10. Yawancin matan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito ya yi magana da su, sun ce ba da saninsu ko amincewarsu aka zubar musu da cikin ba, kuma an ma yi musu barazana da kada su kuskura su fallasa batun.
Rahoton na Reuters ya tayar da jijiyoyin wuya tsakanin al'ummar Najeriya musamman ma su rajin kare hakkin dan Adam, inda suke ganin in dai ya tabbata to lallai an aikata babban laifi. Duk da cewa rundunar sojojin Najeriyar ta karyata wannan rahoton, masu rajin kare hakkin dan Adam da masu kare hakkin mata da yara sun nemi lallai a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin tantance zargin. A cewar Kwamred Lucy Yunana mai rajin kare hakkin mata da yara rahoton ya tayar musu da hankali, kuma ya zama dole hukumomi su gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin ko akasin haka.