Zaben Najeriya da tasirin kungiyoyi
February 12, 2019Daya bayan daya kungiyoyin al’adu da siyasa suka rika bi suna bayyana goyon baya ga masu takarar a zaben shugaban kasar dake tafe a karshen wannan mako, to sai dai shin wannan ya yi tasiri? Kama daga kungiyoyin al’adu irin su Miyetti Allah, ya zuwa masu takama da siyasa, an share tsawon makonnin da suka shude ana baiyyana goyon baya ga manyan ‘yan takarar dake shirin fafatawa a zaben shugaban kasa na ranar Asabar.
A bisa al’ada dai akwai tsamannin tasirin nuna goyon bayan a bangaren masu zaben wadanda ko dai ke zama ‘yan kungiyoyin ko kuma masu goya musu baya. A wasu lokuta ma akan kai har ga bugun kirgin nasarar ta masu takarar nada ruwa da tsaki da irin goyon bayan da suke dashi daga wadannan kungiyoyi dake da tasiri a tsakanin al’ummar kasar: Ko a wannan shekarar ma wasu daga cikin wadannan kungiyoyi sun yi wa masu takarar alkawarin miliyoyin kuri’u dake kwantar da hankula dama kila bugar kirji ga masu fafatwar
To sai dai kuma kasa da mako guda da fara Kada kuri’a a babban zaben Najeriyar daga dukkan alamu ana shirin shan mamakin gaza tasirin goyon bayan kungiya ga makomar masu takara a zabbukan dake tafe.
Ra’ayoyi a tsakanin masu shirin yin zaben dai ya tabbatar da hukuncin ko wanene suke shirin za su zaba din dai na bisa hujjojji daban daban amma ba wai don wani tasiri a tsakanin kungiyoyin dake nuna goyon baya ba.
Bayan kungiyoyin, zamantakewa da ma zumunta a tarrayar Najeriya ta kirkiri al’ada ta kungiyoyin magoya baya dake ikirarin zama sojojin farautar masu zaben amma kuma kan kare tare da komawa dama ta damfara ta siyasa a kasar.