Najeriya: Taimako kan ambaliyar Mokwa
May 30, 2025Mumunan ambaliyar ruwan da ta afka wa garin Mokwa da ke jihar Niger ta fi shafar mata da yara kanana da ruwan mai karfi da aka kwashe fiye da sao'i 24 ana yi ya yi awon gaba da su. Gidaje sama da 3000 sun rushe a yanayin da mutanen da abin ya shafa suka bayyana cewa sun kwashe shekaru rabon da su ga irin wannan bala'i da ya afka masu.
Mokwa gari ne da ke da yawan almajirai da mafi yawancinsu basu da muhalli. Bayanai sun nuna cewa akwai almajirai da dama da ambaliyara ruwan ta shafa, domin akwai kangon da suke fakewa inda sama da almajirai 50 da ke ciki ba'a ga ko da guda daya ba, ana tsoron dukkaninsu sun mutu.
Tuni jami'an hukumar kai daukin gagawa ta jihar Niger suke aikin nemo gawarwakin mutanen da suka mutu wadanda ya zuwa lokacin hada wannan rahoto an samo gawarwakin mutane sama da 100, kuma ana ci gaba da nemo sauran wadanada abin ya yi dalilin mutuwarsu, mafi yawa mata da yara kanana.
Matafiya da ke bin hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya sun yi cirko-cirko saboda ruwan ya shafe gadar da ke hanyar, abinda ya jefa tsoron ko hanyar ta yanke.
Najeriya na fuskantar yawaitar ambaliyar ruwa a 'yan shekarun baya bayan nan domin ko da a wannan shekarar ma'aikatar kula da albarkatun ruwa ta yi garagadin cewa jihohi 31 da kananan hukumomi 148 za su fuskanci ambaliyar ruwa cikinsu har da jihar Niger. A 2024 ne aka fuskanci ambaliya ruwa mafi muni a jihar Borno wacce ta shafi mutane milyan daya da dubu dari biyu.