Najeriya ta zama kasa ta 12 mafi talauci a duniya
June 27, 2025Duk da cewa a kan takarda tarayyar Najeriyar na zaman kan gaba a fannin tattalin arziki a nahiyar Afirka, amma a idanun kwarraru, kasar na zaman ta kan gaba a talauci a duniya baki daya. Wani sabon rahoto na Asusun Lamuni na duniya IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki.
Karin bayani: Nageriya: Barazanar karin matalauta miliyan 13
Bisa karfin tattalin arzikin Dalar Amurka 807, Najeriya na mataki na 12 a cikin kasashe mafiya talauci a duniya baki daya. A cikin kasashe 189 da aka gudanar da bincike a cikinsu, Najeriyar na a mataki na 178, inda ta zarta kasashe irin su Yemen da Sudan ta Kudu da Kwango da Nijar da Sudan, wadanda kusan dukkaninsu ke fama da rigingimu a halin yanzu.
Ana kallon sabon rahoton a matsayin alamun kasawa a bangare na masu mulkin Najeriya da ke fadin cewar suna da burin ceto kasar da ke kara samun nakasu, kamar yadda Ibrahim Shehu, sakataren kungiyar inganta tattalin arzikin arewacin Najeriya ya bayyana.
Karin bayani:Wa ke morar agajin gwamnati a Najeriya?
Akalla Naira tiriliyan 21 ne ake jin matakan gwamnatin kasar guda uku sun samu daga zare tallafin man fetur a shekaru guda biyu. Ko bayan wasu Naira Tiriliyan 96 da masu mulkin na Abuja suka karba da sunan bashi, akwai Naira tiriliyan guda a shekara da masu mulkin ke samu sakamakon ragin tallafi bisa kudin wuta. Sai dai Farfesa Muttaqa Usman, kwarrare a fannin tattalin arziki, ya ce lissafin masu mulkin Najeriya na zaman karatun gizon da baya da tasiri ga rayuwar da ta wuce ta koki.
Karin bayani:Talauci da kashe kudin gwamnatin Najeriya
Miliyoyin 'yan tarayyar Najeriyar na zaman jiran tasirin gobe na shirin da a bana cikin sauyin da gwamnatin kasar ta yi nisa kansa.