Najeriya ta ware makudan kudade don kiwon lafiya
February 4, 2025Kama daga harkoki na lafiya ya zuwa zamantakewada kila ma al‘adu dai Najeriya na karbar gwamman miliyoyi na daloli a shekara cikin suna na tallafi na agaji na kasashe na waje.
A shekaru 22 dai alal ga misali, Najeriya ta karbi agajin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu shida cikin na agaji bisa ciwon Sida daga kasar ta Amurka. Ko bayan wasu dubban miliyoyi na daloli cikin yaki da zazzabin cizon sauro.
Kafin wata barazana a bangare na shugaban Amurka Donald Trump ta shafi daukaci na tallafin na Amurka zuwa kasashe na duniya, tare da dora aya ta tambaya bisa makomar dubban darurruwan da ke dauke da cutar Sidar a Najeriya.
To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce tana shirin yi na gaban kanta, tare da ware wasu dalar Amurka miliyan dubu daya domin harkoki na lafiya cikin kasar.
Ministan lafiya na Najeriyar Farfesa Ali Fate ya ce kasar na shirin daukar nauyin bukatu na lafiyar al'ummarta, maimakon dogaro bisa kasashe na waje.
Akalla Naira miliyan dubu hudu ne dai aka ware domin samar da maganin mutane 150,000 da ke dauke da cutar a karon farko.
Ya zuwa shekara ta 2023 dai an kiyasta 'yan Najeriya miliyan kusan biyu ne ke dauke da cutar Sida, kuma mafi yawa na agajin da suke samu dai na fitowa ne daga kasar ta Amurka.