Najeriya ta lashe kofin kwallon kafa na matan Afirka
July 27, 2025Najeriya ta lashe kofin kwallon kafa na matan Afirka karo na 10 bayan ta doke Morocco da ci 3-2 a ranar Asabar a birnin Rabat na Morocco.
Wannan nasarar ta bai wa kasar zama mafi yawan lashe gasar ta kwallon kafa ta mata a nahiyar Afirka.
Esther Okoronkwo da Folashade Ijamilusi ne suka jagoranci bajintar a filin Stade Olympique na Rabat kafin Jennifer Echegini, wadda aka saka daga baya, ta jefa kwallon na uku da ya bai wa kasar nasara a minti na 88.
Ana wasan cin kofin Afirka na mata a Maroko
Kyaftin din Morocco Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, sun zura kwallaye a farkon rabin lokaci, inda suka bai wa kungiyarsu kwarin gwiwar lashe kofin, to amma sai lamarin ya sauya.
Najeriya ta mamaye wasan daga baya, inda ta rika samun dama daga bugun kusurwa sannan ta rika gasa wa Morocco aya a hannu.
Rawar da ƙungiyar Super Falcons ta Najeriya take takawa
Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya taya 'yan matan murnar wannan nasarar inda ya ce hakan ya nuna irin kokari da jajircewa ne da 'yan Najeriya ke da shi.