Tinubu ya kara yawan kasafin kudin Najeriya
February 6, 2025
Majalisar datawan Najeriyar ta bayyana wannan kari ne a wasikar da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya aika mata inda ya bayyana cewa wata faraga da gwamnatin ta ce ta samu daga haraji ta hanyar ma'aikatun karbara harajin kayayyaki da na shige da ficen kayayyaki.
Karin Bayani: Shugaban Najeriya ya gabatar da kasafin kudi
Najeriya dai ta kara kasafin kudin na wannan shekara ce wanda ke da wagegen gibi na kimanin Naira tirliyan 13, gibin da gwamnati ta bayyana cewa sai ta ciwo bashi domin aiwatar da kasafin kudin. Mece ce dubarar wannan kari bisa halin da tattalin arzikin ke ciki?
Kodayake gwamnatin ta bayyana cewa zata yi amfani da wannan kari ne domin bunkasa harakar hako ma'adananj karkarkashin kasa, da noma rani tare da kara jari a bankin bai wa manoma bashi. To sai dai ba kasafai ne dai ake samun irin wannan hali ba inda bayan an yi nisa da aiki a kasafin kudin da aka Makara wajen kamala tantance shi maimakon shirya dan karamin kasafin kudi kamar yadda aka saba.
Najeriya ta dade tana fuskantar matsalar kasa aiwatar da kasafin kudinta baya ga gibin da yake fusknata tare da ci gaba da karbo bashi daga kasashen wajen domin cike gibin da ake da shi a kasafin kudin da yake dama can hasashe ne na kudadden da za'a samu.