Najeriya ta kara jaddada bukatar sakin Bazoum
April 11, 2025Ministan sadarwar Najeriya Mohammed Idris a wata hira da ya yi da kafar talibijin din France 24, ya ce suna bukatar a saki Bazoum da iyalinsa tun da dai bai babu wani laifin da ya aikata.
Najeriya wace yanzu haka ke rike da shugabanci na karba-karba na kungiyar ECOWAS ta sha alwashin ci gaba da matsawa sojojin lamba har sai sun sako bazoum da ake tsare da shi a fadar mulki ta Yamai tun a ranar 26 na watan Yulin shekarar 2023.
Dangantaka a tsakanin Najeriya da Nijar ta yi tsami tun bayan kifar da halastaciyar gwamnatin farar hula ta Bazoum, wanda Abuja ta yi barazanar daukar matakin soji a kansu lamarin da ya dagula dadaddiyar alakar dake tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna.
A yan kwanakin baya nan ne sojojin a Nijar suka saki wasu fursunonin siyasa sai dai babu batun Bazoum da mai dakinsa.
Karin Bayani: Rashin armashin sakin fursunonin siyasa a Nijar