Najeriya ta daukaka kara kan Nnamdi Kanu
October 21, 2022Talla
Gwamnatin Najeriya ta garzaya kotun koli inda take kalubalantar wanke jagoran kungiyar IPOB ta masu rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu da wata kotun daukaka kara ta yi.
A makon jiya ne dai aka wanke Nnamdi Kanu daga zarge-zargen ta'addanci da gwamnatin Najeriya ke yi masa, inda kotun ta ce gwamnati ba ta bi hanyoyin da suka dace wajen taso keyar Kanu daga Kenya zuwa kasar da aka yi a baya kafin a tsare shi ba.
Da ma gwamnatin Najeriyar ta ce tana nazarin matakin da za ta dauka a kan hukunncin inda a yau Juma'a lauyoyinta suka tabbatar da kai maganar gaban kotun na koli.
Har yanzu dai ana ci gaba da tsare jagoran na IPOB Nnamdi Kanu a gidan yari, duk kuwa da wanke shi da kotun ta yi.