Najeriya ta dakile fataucin tsuntsaye sama da 1,500
August 6, 2025Cafke tsuntsayen da aka yi yunkurin fitar da su ba bisa ka'ida ba na daga cikin dakile fataucin dabbobi mafi girma a Najeriya, a cewar mai magana da yawun kungiyar kare hakkin dabbobi ta yammacin Afirka Mark Ofua kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Karin bayani:Najeriya ta lalata hauren giwaye na miliyoyi
Hukumar Kwastam a Najeriya ta ce an cafke mutanen da suka yi yunkurin fitar da tsuntsayen na Aku da Kanari masu launuka daban-daban na shudi da rawaya har ma da ruwan dorawa zuwa kasar Kuwait a ranar 31 ga watan Yuli.
Karin bayani: Nijar: Cece-ku ce kan dokar haramta fitar da dabbobi waje
Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar haramta fataucin dabbobi da kuma halittun da suka dauko hanyar karewa a duniya.