Najeriya ta bijire wa muradin Amurka
July 11, 2025Tuggar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Najeriya a ranar Jumma'a, inda ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, yana kokarin tilasta wa kasashen Afirka karbar ‘yan Venezuela da aka kama da laifin zama a Amurka ba bisa ka'ida ba.
Ministan ya ce kimanin mutane 300 ciki har da wasu masu laifi da aka fito da su daga gidajen yari shugaban na Amurka ke son Najeriya ta karbe su, yana mai cewa baya ga Najeriyar akwai wasu karin kasashen Afirka da shugaba Trump ke bukatar su ma su karbi bakin hauren na Venezuela.
Babban jami'in diflomasiyyar Najeriyar ya ce kasarsa na fuskantar nata matsaloli masu nauyi, don haka ba za ta iya daukar nauyin wani karin kalubale ba, yana mai fargabar idna har Najeriya ta karbi wannan bukata ta bude kofar bai wa murkan damar jibge mata bakin haure a kasarta.