Najeriya: Shirin sauya tunanin barayin daji
February 14, 2025A wani abun da ke zaman kokarin sauya tunani, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon shirin sauya tunanin dubban barayin dajin da suka addabi sashen arewa maso yammacin kasar
Daruruwan barayin daji da iyalansu ne dai jami'an tsaron kasar suka ce suna fatan sake tsugunarwa a karkashin shirin da ya shafi jihohin Katsina da Sokoto da Zamfara da Jihar Kebbi.
Akalla barayin daji 30,000 ne gwamnatin kasar ke fatan iya yadda kwallon mangoro da kila rungumar zaman lafiya da rayuwa mai inganci a cikin yankin da ke zama kan gaba cikin batun talauci a cikin tarrayar Najeriyar.
Tun daga shekarar 2019 ne dai aka fara ganin ta'azzara ta ayyukan barayin dajin da suka sace mutane kusan dubu 10,000 tare da raba sama da 700,000 da muhallansu.
Bayan kisan da daman gaske na shugabanni da kila ma mabiyansu, daga dukkan alamu ana ganin karuwar barayin dajin da ke tunanin mika wuya da ajiye makamai a yankin a fadar Munnir Fura Girke da ke bin diddigin batun tsaro a yankin.
‘‘Najeriyar na fatan dorawa bisa nasarar gwamnatin kasar da ta kalli sake tsugunar da ma samun aiki ga daruruwan yayan kungiyar Boko Haram".
A shekarar 2016 ne dai Abujar ta kaddamar da shirin da ke zaman wani bangare na lallashi a cikin neman kare ayyukan ta‘addar.
Bayan da kasar ta bada dubban miliyoyin daloli a yaki da ta‘adda amma kuma ta kasa kai wa ga murkushe aiyyukan 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram.
Akasin akidar da ake ta'allakawa da ayyukam Boko Haram batun talauci a yankin arewa maso yammacin kasar ne ke zaman kan gaba a ayyukan barayin da suka yi tasiri ga rayuwa da makomar al'ummar yankin.
Abun kuma da ya sa ake ganin zai yi wuya iya tabbatar da kaiwa ga sauya tunani da kila ma lallashin kai wa zuwa tabbatar da sauyi na rayuwa.
To sai dai kuma sabon shirin na iya sauya da dama a cikin yankin in har an tabbatar da amana a tunanin Dr Yahuza Getso da ke sharhi cikin batun tsaron.
Koma ya zuwa ina ake shirin a kai a kokarin samar da amanar, batun kasa kai wa ga amanar ce yanzu haka ke neman mamaye rawar kungiyoyin sa kai a kokarin zaman lafiyar al'ummar tarayyar Najeriyar.
Zargin da wani dan majalisar wakilan Amurka Scott Perry ya yi bisa rawar cibiyar agajin Amurka wajen daukar nauyin Boko Haram ne ke neman yamutsa hazo cikin kasar a halin yanzu.
Perry dai ya zargi kungiyar USAID da daukar nauyin Boko Haram da ma ragowar kungiyoyin ta'addan da ke tada hankali a sassa daban daban na duniya.
Faruk B B Faruk mai sharhi kan siyasar yankin kuma yace biri yana kamar mutum jela ce ya rasa.
Batun lafiya a Najeriyar dai na zaman na kan gaba cikin fatan gina ingantaccen tattalii arziki da kila walwala tsakanin al'umma.