A bana ne Imam Nuraini Ashafa da takwaransa Fasto James Wuye suka cika shekaru 30 da fara aikinsu na sasanta mabiya addinai dabam-dabam a Najeriya da nufin wanzar da zaman lafiya, aikin da suka ce sun cimma nasarori da dama a tsukin wadannan shekaru.