Samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya
September 15, 2022Gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar 19 da daukacin manyan sarakunan yanka na yankin, sun aminci ne a karo na farko kan batun samar da 'yan sandan mallakar jihohin domin magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin. A baya dai gwanonin sun sha hawa kujerar na ki kan duk wata shawarar samar da 'yan sanda mallakar jihiohin domin magance tabarbarewar tsaro a kasar, abin da tuni takwarorinsu na kudancin kasar suka yi ta gwagwarmayar ganin an tabbatar. Masana da masharhanta gami da talakawa sun bayyana fahimtarsu kan abubuwan da ya sa gwamnonin suka dauki wannan mataki, wanda yawanci suka ce matakin ya daure musu kai.
Sai dai kungiyoyin matasan arewacin Najeriya, na ganin gwamnonin sun tsaga sun ga jini ne ganin tasirin da wasu al'umma suka yi a taimakawa jami'an tsaro a yaki da ta'addanci musamman ma a yankin Arewa maso Gabashin kasar. Masana kamar Manjo Shu'aibu Galma mai ritaya na ganin gwamnonin sun dauki wannan mataki ne, saboda ganin takwarorinsu na kudancin kasar sun kafa rundunonin tsaro kuma suna samun nasarar magance matsalolin tsaron. Yanzu haka dai al'ummar kasar sun tsayar da hankalinsu wuje guda domin jin mataki na gaba, bayan baki daya gwamnonin Najeriya 36 sun amince da samar da 'yan sandan jihohin. Al'umma dai na fatan za a dauki mataki na bai daya, domin samar da hanyar da za a magance matsalolin tsaro da ya addabi kasar baki daya.