Kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aiki
November 6, 2018Matakin dakatar da yajin aikin dai ya biyo bayan cimma yarjejeniya da gwamnati dangane da batun mafi karancin albashi. Sakatare janar na kungiyar kwadagon Najeriyar NLC, Peter Ozo-Eson ya shaidawa manema labarai cewa, bayan kwashe tsahon yinin Litinin biyar ga watan na Nuwamba suna tattaunawar da ta kai su har cikin dare, gwamnatin ta amince da ta biya mafi karancin albashi na Naira 30,000 duk wata ga ma'aikata, abin da ya dara naira 18,000 da ake bai wa ma'aikatan duk wata a matsayin mafi karancin albashi a yanzu haka. Ozo-Eson ya kara da cewa yarjejeniyar da suka cimma tare da ministan kwadagon kasar Chris Ngige za a mika ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan Talatar shida ga watan na Nuwamba. Ozo-Eson ya nunar da cewa za su ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana, ko bukatar sake daura damarar daka yajin ka iya tasowa.