Najeriya na shirin rage cunkoso a gidajen gyaran hali
October 10, 2022Dabara ce dai da gwamnatin kasar ke son bi a kokarinta na rage mugun cunkoson da take fuskanta a gidajen yarin kasar, inda ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriya, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana wannan shiri. Wannan ci gaba ne daga shirin da Najeriya ta fara aiwatarwa a kan rage cunkoson gidajen yarin ta hanyar yi ma wasu afuwa da ta yi a watanin baya.
Abin damuwa a kan daukacin lamarin shi ne, kashi 90 cikin 100 na fiye da fursunonin dubu 75 da ake tsare da su a gidajen gyara halinka na Najeriyar, suna jiran shari'a ne, abin da ya haifar da cunkoso a gidajen maza na kasar. Mallam Auwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar CISLAC ya ce sun yi marhabin da matakin.
Malam Abubakar Umar shi ne jami'in yada labaru na hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya, ya ce wasu tsare-tsare da suke da su a gidajen na taimaka wa fursunoni koyon sana'oi da ma karatu.
Kokari na rage cunkoso a gidajejn yarin da ma rage kashe kudadde na kula da daurarrun muhimi ne a wannan mataki da ma halin da Najeriyar ke ciki.
Dr. Abubakar Umar Kari na mai bayyana bukatar daukar sabon salo na kula da masu aikata laifuka inda ya ce ba dole ba ne sai an sanya su a gidajen yarin ba.
Ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriyar ya ce zai tuntubi gwamnonin jiho a kan wannan shiri domin rage cunkoso a gidajen yari har 253 da ake da su a Najeriyar, domin akasarin fursunonin da ake tsare da su, mutane ne da suka karya dokokin jihohi, ba na tarayya ba.