Najeriya: Miliyoyin yara na fama da rashin ruwa
March 22, 2021Wannan adadi na yara kananan da asusun kula da lafaiyar yara na Majalisar Dinkin duniyar ya fitar, ya nuna cewa kashi 29 cikin 100 na adadin yara kanana da ke Najeriyar ne ke cikin wannan hali na karancin ruwa a kasar, abin da ke cikin bincike mai zurfi ne da aka gudanar a kan alakar talauci da karancin ruwa a tsakanin al'umma.
Bayani ya nuna cewa yara milyan 26.5 na daga cikin adadin ‘yan Najeriya sama da milyan 70 da ke fuskantar karancin ruwan sha kamar yadda Dr Uba Lawal, jami’i mai kula da harkokin ruwa a Asusun Kula da Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Najeriyar ya nunar.
An dai kai mataki na nuna damuwa a kan illar da wannan ke da shi ga rayuwar al'umma a Najeriyar, musamman ma dai yara kanana, da matsalar rashin samun ruwa duk da wadatarsa a karkashin kasa a Najeriyar ke kara tazara.
A shekarar da ta gabata ce dai Najeriyar da hadin kan UNICEF suka kadammar da nazari a kan batun samar da ruwan sha a kasar, wanda UNICEF ta ce duk da samun ci gaba amma da sauran aiki a gaba.
Najeriya dai na fatan samawa kashi 70 na al'ummarta ruwan sha mai tsafata to sai dai akwai kalubale babba na gurbacewar ruwan da a yanzu gwamnatin ke yaki da shi ta hanyar rage yawan masu bayan gida barkatai a kasar.