Najeriya: Makomar shirin bai wa dalibai bashin karatu
May 2, 2025Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya ICPC dai ta ce kusan kaso 70 cikin 100 na kudaden basu isa zuwa ga daliban da ake fatan su ci moriyarsu cikin shirin da ke zaman gada tsakanin talakwa da karatun zamani.
A mako mai zuwa ne dai aka tsara wata ganawa da shugabannin jami'o'in tarayyar Najeriya da ita kanta hukumar rancen na dalibai a karkashin jagorancin ministan ilimi na kasar da nufin tantance abin da ke faruwa cikin shirin rancen na dalibai.
Tun farko hukumar yaki da cin hanci ta kasar ce dai ta yi zargin wasoso da kudaden rancen, inda ta ce an kwashe mafi yawa na kudaden da aka tsara cikin shirin da ke da burin ceton ilimi a kasar.
Daga kusan Naira miliyan dubu 200 da Abujar ta saki, abin da hukumar bashin ta bayar bai wuce Naira miliyan dubu 44 ba.
Ana dai zargin wasu a cikin makarantun da rike kudaden rancen na dalibai a bankuna da niyyar neman kudin ruwa, ko kuma kwashe wasu cikin kudaden.
Wani dalibi da bai so a ambaci sunansa ya ce an rike masa jarrabawa sakamakon rashin sakin kudin bashin da ya nema.
A shekarar 2023 ne dai gwamnatin Najeriyar ta bullo da shirin da ke da babban burin tallafa wa dalibai marasa karfi bayan da gwamnatin kasar ta kara kudade ga jami'o'In kasar.
Shirin kuma da kungiyar malamai na jami'o In tarayyar najeriyar ASUU tace ba'a bukatarsa.
Akwai dai tsoron rushewar tsarin na iya shafar karatun dalibai da dama a jami'o'in kasar wadanda bayan bullar shirin suka rika kara kudaden makaranta ga dalibai.
Da kyar da gumin goshi ne dai mafi yawan daliban ke iya kai wa ga biyan dubban daruruwan Nairori na kudaden makaranta.
Rashin isassun kudade, ko bayan ko in kular yan mulki ne dai ake ta'allakwa da batun lalacewar ilimi a cikin tarayyar Najeriyar.