Najeriya: Majalisa ta bukaci sauya hafsoshin soja
January 30, 2020'Yan majalisar dokoki a Najeriya sun bi sahun masu kiraye-kiraye ga shugaban kasar kan ya salami manyan hafoshin kasar wadanda ba tun yau ba wa'adinsu na tafiya ritaya ya cika. Tuni kuma batun ya fara fuskantar martani daga wasu 'yan kasar ta Najeriya a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke neman su gagari kundila a kasar.
Ba tare da wani luge-luge ne ba 'yan majalisar kasar ta Najeriya suka fito suka bayyana bukatar ganin manyan hafsoshin Najeriyar su yi ritaya ko kuwa shugaban kasar ya sallame su. 'Yan majalisar na danganta ci gaba tabarbarewar tsaro da kasar ke fuskanta da yadda shugaban kasar ke ci gaba da yin riko da wasu manyan hafsoshin sojin kasar da ya kamata su tafi ritaya a maye gurbinsu da sabbi.
'Yan majalisar dokokin wakilan Najeriyar dai sun kwashe awoyi suna tafka zazzafar muhawara kafin kai wa ga daukar wannan mataki.
A majalisar datawan Najeriyar ma dai batun ya dauki hankali da ma haddasa tayar da jijiyoyin wuya, a kan batun rashin tsaron da suka ce ba za su saka idanu suna kalon abin da ke faruwa ba tare da daukar wani mataki ba. Ta kai ga shugaban marasa rinjaya Sanata Eyinnaya Abaribe kiran shugaban Najeriya da ya yi murabus, furucin da amma ya haddasa hatsaniya a majalisar da ma mayar da martanidaga wasu takwarorinsa na majalisar.
An dai dade ana kace-nace a kan wannan batu na barin hafsoshin tsaron Najeriyar su ci gaba da rike mukammansu, lamarin da wasu 'yan kasar ake ganin ya saba wa dokokin kasar
Yanzu haka dai a daidai lokacin da 'yan kasar ke kashe kunne su ga amsar da shugaban kasar ta Najeriya zai bayar ga wannan bukata ta 'yan majalisu da ma wasu 'yan kasar ta ya sallami manyan hafsoshin soja na kasar, Shugaba Muhammadu Buhari ya bude a birnin Abuja wani zaman taro kan harakokin tsaro inda ake sa ran zai bayyana matsayinsa kan wadannnan kiraye-kiraye da ake yi masa.