Najeriya: Kokarin kafa jam'iyyar ADA don kalubalantar APC
June 23, 2025Wasu dai na zargin aro na yawu kan hanyar neman samu na rijistar All Democratic Alliance da ke zaman sabuwar kafa ta masu adawar. Tuni dai suka ce sun isa hedikwatar hukumar zabe da nufin neman kafa wata jama'iyyar da ke da babban fatan kwace mulki a cikin tarayyar Najeriya.
Kuma ko bayan tsawo na lokaci ana ta hasashe, daga dukkan alamu All Democratic Alliance na zaman kafa cikin sabon fatan kai APC cikin gidan tarihi. An dai ambato manya cikin gidan na adawa irin nasu Atiku Abubakar da Rotimi Ameachi, da Nasiru El Rufa'i a kokari na rushe tsarin na tsintsiya, a karkashin tsarin ADA.
Bullar All Democratic Alliance cikin fagen na siyasa dai na zaman babbar dama ga masu adawar cikin tunanin sauyin tarayyar Najeriyar.To sai dai kuma sabuwar kungiyar ta siyasa na zuwa ne kasa da shekaru biyu da babban zabe.
Karin bayani: Ko hadakar jam'iyyun adawa ne mafitar Najeriya?
A cikin wannan mako ne dai ake sa ran fitar da sunaye na shugabannin ADA a matakai daban daban cikin kasar. To sai dai kuma daga dukkan alamu kalubalen da ke gaban jam'iyyar na zaman kauce wa buri da kila kallo na makoma ta siyasa da kila ma kasa.
Majiyoyi a sabuwa ta kungiyar dai sun ce ana kiki kaka bisa batu na shugabancia tsakanin tsofaffi na jini da kuma matasan dake hankoron dauka zuwa gaba. Ita kanta sabuwar jam'iyyar dai a tunanin Solomong Dalung dake zaman jigo cikin adawa ta kasar bata samu amincewar masu adawar tarayyar najeriyar ba ha rya zuwa yanzu.
Karin bayani: Najeriya: Rikicin jihar Rivers ba ta sauya zane ba
To sai dai kuma ko ya take shirin kayawa bisa batun banbancin, ADA dai na da jan aikin tsallake siradi na hukumar zabe ta kasar mai zaman kanta ta INEC. Akwai dai tsoron toshe masu adawar a bangaren masu mulki na kasar.
Can cikin gidan tarihi dai, APC na zaman jam'iyya daya tilo da ta yi nasarar karbe iko a cikin kankanin lokaci da kafa ta. Akwai dai tsoron rabuwa ta adawa a lokacin da jam'iyyar APC ke hadiya dai na zaman barazana a tsakanin masu adawar da kaiwa ya zuwa cika burin na su.
Abun jira a gani dai na zaman iya kaiwa ya zuwa hadiye burin a cikin fatan sauyin da ke zaman gada tsakanin adawar da kauce wa komawar kasar zuwa jam'iyya daya tilo.