Ko ya ya zaben 2027 a Najeriya zai kaya?
July 1, 2025Daukar wannan matakin da gamayyar 'yan adawar Najeriyar suka yi, na zuwa ne sakamakon tababar samun yi wa kungiyar siyasa ta ADA rijista da suka gabatar a gaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC a daidai lokacin da ake koken jamiyyun Najeriyar sun yi yawa sosai. Sun dai fara ne da tunkurar jamiyyar SDP, inda har wasu daga cikin jagororin wannan tafiya ta kafa babbar jamiyyar adawa daya tilo a Najeriyar kamar tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai suka kai ga shiga jam'iyyar, kafin tafiyar ta waste da SDP da a yanzu ke cikin rigingimu.
Karin Bayani: Najeriya: 'Yan sanda sun mamaye ofishin PDP
Daga bisani sun kafa kungiyar siyasa ta All Democratic Allaiance tare da mika bukatar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC ta yi masu rijista, kafin a yanzu su ayyana darewa bayan jamiyyar ADC a kokarinsu na tunkarar zaben 2027. To sai dai ga Dakta Yunusa Tanko jigo na jam'iyyar Labour daya daga cikin jam'iyyun da ke kokarin yin hadakar da su, ya bayyana cewa akwai sarkakiyar tattare da lamarin musamman ma bayanan da Hukumar Zabe ta yi.
Tsoro ko fargabar samun rijista a kan lokaci babban al'amari ne, duk da cewa hukuma ce mai cin gashin kanta bisa manufa amma bukatar neman rijistar ya zo a daidai lokacin da wa'adin shugabanta ke gab da cika. Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC, ta bayyana cewa mafi yawan kungiyoyin siyasar da suka nemi a yi masu rijista ba su cika ka'idojin da ake bukata ba.
Karin Bayani: Me ya sa kalaman Tinubu ya harzuka jam'iyun adawar Najeriya?
Daukar dogon lokaci ana wannan tirka-tirka ta kokarin samar da babbar jam'iyyara dawa daya a Najeriyar da rigingimun da suka addabi jam'iyyun adawar kasa da shekaru biyu a gudanar da zaben 2027, na jefa shakku a kan katabus din da bangaren 'yan adawar kasar da tasirinsu ya ragu ainun a fagen siyasar Najeriyar za su iya yi. Kwararru a fanin kimiyyar siyasar Najeriyar na bayyana jam'iyyar ta ADC a matsayin wacce ba ta da koda kansila da aka zaba a karkashinta, abin da ke jefa shakku a kan rawar da za ta iya takawa a zaben na 2027.