Najeriya: Kaura don neman lafiya a kasar waje
July 17, 2025Akalla likitoci kusan 16, 000 ne suka bar Najeriya da sunan cin rani, a shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata.
Ya zuwa 2024 kadai manyan Najeriya suka kashe abun da ya kai dalar Amurka miliyan 40, 000 a shekaru 10 cikin neman magani a kasashen waje a cewar babban banki na kasar. Hujjojji iri iri ne dai kan kai manyan tarayyar Najeriyar zuwa neman magani a kasashen waje.
Dr Umar Tanko kwarrare ne a fannin lafiyar al'umma da kuma ya taka rawa wajen zama likitan manya a kasar. Shi ma Mohammed Auta da yake zuwa Dubai domin duba lafiyarsa ya ce dole ce ta kai shi neman magani a wajen kasar.
Su kansu masu mulkin kasar daga dukkan alamu na dada janyewa cikin batun imani kan tsarin lafiya na tarayyar Najeriyar.
Kama daga marigayi Umar Musa Yar Adua, ya zuwa Buhari ko bayan shi kansa shugaban da ke kan mulki, asibitocin waje ne ke zaman wurin zuwa ga shugabannin Najeriya cikin batu na lafiyar
Ana kuma zargin likitocin kasar da kasa nuna sadaukarwar da ta zamo uwa makarbiya a kokarin gina su.
Tarayyar Najeriyar dai ta na kashe tsakanin dalar Amurka 21, 000 zuwa 51, 000 wajen horar da kowane likita a jami'o'i mallakiar gwamnatocin kasar.
Najeriyar dai ta na da bukatar ware abun da ya kai kaso 15 cikin dari na daukacin kasafin kudin kasar a shekara, kan sake gina asibitoci da ragowar cibiyoyin lafiya.