Najeriya: Karin albashi ga masu mukaman siyasa
August 19, 2025Tun a shekara ta 2008 ce dai masu siyasar suka kalli karin karshe kan albashin nasu, kuma hukumar ta ce kudaden da suke karba a halin yanzu sun yi kadan su tabbatar da sauke amanar da ke kansu.
Ya zuwa yanzun dai shugaban kasar na daukar albashin da bai wuci Naira Miliyan daya da rabi ba a duk wata. A yayin da ministocinsa ke daukar kasa da Naira miliyan daya a matsayin albashin. Adadin kuma da a cewar hukumar sanya albashin masu rike da mukaman siyasa bai zo dai dai da tunanin zahirin da ake ciki a kasar a halin yanzu ba.
Shugaban hukumar tsara albashin Mohammed Shehu, ya ce ba dai dai bane gwamnan babban banki ya nunka shugaban kasa albashi har sau 10.
Karin Bayani:Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi a Najeriya
Hukumar ta ce tana tunanin karin albashin domin iya bayar da damar sauke nauyin da ke wuyan jagororin da ke tafi da harkokin kasar.
Duk da cewar dai hukumar bata kai ga ambato lokacin yin karin da kuma yawan albashin ba, tuni sabuwar sanarwar ta fara tada hakarkari wuyai a tarayyar Najeriyar
A bangaren 'yan kungiyar kwadago dai tuni sanarwar ta kai ga tada jijiyar wuya inda ma'aikatan suke fadin ba hali a cewar Comrade Abbayo Nuhu sakataren kungiyar manyan ma'aikatan kasar TUC.
In har tayi baki a tunani na jan wuya cikin tsarin aiki, ga ragowa na kananan ma‘aikata, tunanin karin ya saba da hankalin dake cikin tsrain aiki yanzu.
Duk da cewar majiyoyin gwamnatin sun ki su ce uffan kan bukatar karin, korafi cikin gidan na masu rike da mukaman siyasa na zaman Naira miliyan daya a wata bata isa kama gidan haya da man mota ba, balle batun karatu da ma na lafiya ta iyali.
Karin Bayani:Najeriya: Kokarin shawo kan matsalar tsadar rayuwa da kuncin jama'a
Yawan ma'aikatan da ke mata aiki dai ya sa Najeriya shiga tsakanin kara yawan albashi na yan kasar da gaza sauke nauyin ginin kasa da ke nuna alamun gagarar kundila.
Dr Isa Abdullahi dai kwararren masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce ana bukatar kallon tsaf a kokarin burge 'yan siyasar.
Sau uku hukumar tana yunkurin neman karin albashi cikin gidan siyasar, sau uku kuma tana fuskantar fushin masu zuciyar mai tsumman da ke fadin ba hali.
A shekarar 2008 dai gwamnatin kasar ta yi karin karshe na albashin yan mulkin, karin kuma da ya haifar da hauhawar farashi da kila sauyin bukatu cikin kasar a halin yanzu