Najeriya: Kalubalen sauyin sheka ga Jam'iyyar PDP
April 29, 2025Tsoro ko firgita shi ne halin da jamiyyar PDP ta shiga da ya sanya jiga-jigan jam'iyyar a karkashin kwamitin gudanwarta haduwa a hedikwatar jamiyyar a kokarin nemo mafita daga guguwa da ke neman yin awon gaba da yayan jamiyyar kama daga gwamnoni zuwa 'yan majalisar dokokin tarayya da ma matakai na kanana hukumomi domin sauya sheka
Duk da cewa kusan shekaru biyu kenan rabon jamiyyar ta PDP da ta samu zaman lafiya bayan da ta sake shan kaye a babban zaben Najeriyar a 2023, jamiyyar bata taba fuskantar barazana irin wannan ba tun 1998 da aka kafa jamiyyar. Shugaban jamiyyar Umar Iliya Damagum ya ce sun mika al'amarinsu ga Allah kuma suna da kwarin gwiwa.
An kai ga shiga zargi na wasu yayan jamiyyar da yi mata kafar ungulu wadanda ake ganin sun raba kafa, suna a cikin jamiyyara amma ana ganinsu tare da jamiyya mai mulki. Wannan na daya daga cikin batutuwan da taron kwamitin gudanarwar jamiyyar ya ke kokarin shawo kansa. Sai dai ko za su iya tasiri a yunkuri da mutane da dama ke ganin kamar sun so su makara.
Duk da wannan A yanzu ana ta samun sabanin ra'ayi tsakanin masu yunkurin a samar da babbar jamiyyar dawa daya tilo inda shugaban gwamnonin jamiyar Bala Mohammed ya ce a hir, shi kuma dan takarar Jam#iyyar na shugaban kasa Atiku Abubakar ke nuna inda hankalinsa ya karkata.
A yayin da wannan ke faruwa ana jin baraka ta kuno kai a tsakanin shugaban gwamnonin na PDP Gwamnan Bauchi Bala Mohammed da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a kan yunkurin kafa babbar jamiyya daya ta 'yan adawa.
Shugabanin jamiyyar PDP dai na kokari na kama-kama don shawo kan matsalolinsu na cikin gida tare da toshe duk wata kafa da ke sanya yayanta ficewa daga jamiyyar domin gudun a yi mata tashin balbale, domin tun kafin taron kwamitin gudanarwar sai da wasu 'yan kwamitin datawan jamiyyar suka kwashe lokaci mai tsawo suna ganawa da shugaban jamiyyar a Abuja.