Kalubalen jihohin Najeriya kan karin albashi
February 10, 2025Can cikin batu na takarda dai, jihohin Tarayyar Najeriyar 36 na ganin karuwar yawan kudin shiga sakamakon zare tallafin man fetur da ma uwa uba rushewar darajar Naira ta kasar. Kuma ko cikin watan Disambar da ya gabata dai, jihohin sun karbi abun da ya kai Naira miliyan dubu 498 a matsayin kason arzikin kasar. To sai dai kuma a zahiri jihohin Najeriyar na kara talaucewa, tun bayan karin mafi karancin albashi a kasar.
Karin Bayani: Najeriya: Kokarin shawo kan matsalar tsadar rayuwa
Ya zuwa yanzu dai, yawan kudin albashin ya karu da kaso kusan 90 bisa abun da suke biya a baya. A kalla jihohi 27 ne dai ke zaman jiran kudin tarayyar, kafin sauke nauyin albashin maimakon 24 da ke cikin wannan yanayi ya zuwa mayun bara. Wanna dai na dada nuna irin jan aikin da ke gaban kasar da ta zare tallafin man fetur a cikin neman mafita, amma kuma ke fuskantar karuwa ta rudewar lamura.
#b#Ibrahim Jibo dai tsohon kwamishin kudi da tsara tattalin arziki ne a Zamfara, kuma ya ce dambu ne ya yawan da ba zai iya jin mai ba a jihohin kasar. Duk da karuwar yawan kudin albashin, ana kuma zargin karuwar halin bera a da dama cikin jihohin kasar yanzu haka. Kuma faduwa ta amanar ce ta kai jihohin kasar cikin halin rudu, a tunanin Farfesa Muttaqa Mohammed Usman da ke zaman kwararre kan batun tattali na arzikin kasar.
Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta zargi 'yan kwadago da zagon kasa
Rikicin karuwar talaucin dai, na zuwa a lokacin da majalisar tarayyar kasar take tunanin kara yawan jihohi. Duk da cewar dai ana kiran batu na damar kari na fada, Najeriyar a tunanin Dakta Faruk BB Faruk na tsakiyar gazawar jihohin ne sakamakon baro gini tun ranar zane. Ya zuwa watan da ya shude dai jihohin Legas da Kaduna da Abia da Benue da Enugu da Ogun da Jihar Niger da jihohin kwara da Osun ne suke iya biyan mafi karancin albashin, ba tare da fuskantar taskun jiran daukin tarayyar ba.