Jirgin kasa ya yi hadari a tsakanin Abuja da Kaduna
August 26, 2025Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa wani jirgin kasa dauke da fasinjoji da ya taso daga Abuja babban birnin Tarayya ya yi hadari a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna a safiyar Talatar nan, lamarin da ya yi matukar tayar da hankalin fasinjoji da kuma 'yan uwansu.
Har kawo wannan lokaci ba a fayyace takamaiman abin da ya jawo hadarin jirgin kasan ba, kuma babu wani rahoto daga hukumomi dangane da mutuwa ko kuma jikkatar fasijojin ba.
Majiyoyin masu tushe daga Najeriya sun bayyana cewa an tura bataliyar sojoji zuwa wurin da hadarin da auku domin taimakawa jami'an agaji wajen kwashe fasinjojin da suka makale a cikin jirgin kasan a lokacin da ya sauka daga kan layin dogo.