Yan bindiga sun hallaka babban limamin Coci
January 16, 2023Talla
Gwamnatin Italiya na daga cikin kasashen yamma da suka yi Allah-wadai da kisan Ravaran Isaac Achi, wani babban limamin Cocin Katolika da ke jihar Neja a arewacin Najeriya, wasu 'yan bindiga da kawo yanzu ba a iya ganosu ba, sun kai hari kan gidan limamin a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka kone gidan bayan da suka gagara shiga, sun kuma harbi wani limami da suke zaune tare a kafada a yayin da ya ke kokarin tserewa.
Al'amarin ya auku ne a garin Paikoro da ke jihar ta Neja mai fama da aiyukan 'yan bindiga. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da gomman masu ibada a wata mujami'ar Katolika a yankin Kankara da ke jihar Katsina a arewacin Najeriyar.